Wassawa ya shedawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewa yayi matukar farin ciki da wannan mafarki nasa ya zama gaskiya bayan da hukumar FIFA ta kammala tantance shi a ranar Lahadin nan.
Wasswa wanda ya shugabanci kulub din Uganda crane a gasar cin kofin kwararru ta Afrika a shekarar 2014 a Africa ta kudu, tun daga wancan lokacin baya tare da kowane kulub din wasa, bayan da ya bar kulub din na Uganda side SC Villa a gasar Firemiya.
Shidai kulub din Iraq Al Shorta SC yayi nasara har sau biyar a gasar wasannin Firemiya, a kakar wasanni ta 2012/13.
Dan wasan a yanzu haka, ya lashi takobin ci gaba da shiga harkokin wasannin kwallon kafa gadan gadan.
Wasswa, ya koma Uganda ne a shekarar 2011, bayan da aka tsare shi a filin jirgi na Ataturk na kasar Turkish bisa samunsa da wasu haramtattun kwayoyi, al'amari yayi sanadiyyar aka garkameshi a gidan yari, kuma wannan lamari yayi sanadiyyar soke kwantiraginsa da Kardemir Demir Celik Karabukspo.
Baya ga irin wasannin da ya buga a Turkiyya, Wasswa ya buga wasan kwallon kafa na kwararru a da kulub din St George na Habasha da kuma FC Cape Town na Afrika ta kudu.
Bugu da kari, ya buga wasa a KCCA FC da SC Villa a wasannin Premier League na Uganda.(Ahmad Fagam)