in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Maradona: Zan amince na taka leda tare da Tevez
2016-01-20 08:59:48 cri
Fitaccen dan wasan kwallon kafar nan na kasar Agentina Maradona ya fada a Litinin din nan cewar zai iya buga wasa tare da Carlos Tevez a kulub din Boca Juniors.

Dan wasan wanda ya samu nasara a wasannin cin kofin duniya a shekararun 1986, ya samu daukaka a matsayin fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya, ya wallafa a shafinsa na Facebook inda yake nuna cewa Tevez yana sanye da kayan 'yan wasan kulub din na Boca.

A saman hoton ya rubuta cewar: "Zan iya buga wasa tare da Carlitos a Boca".

Sama da masu mu'amala da shafin Facebook dubu 100 ne suka nuna sha'awa ga rubutun cikin sa'a guda.

Shidai Tevez yayi nasarar zara kwallaye sau 17 a wasanni dabam dabam da ya buga daga lokacin da ya fara aiki da kulub din zuwa watan Yuni. Ya taba taimakawa Buenos Aires outfit ta Argentine tayi nasara a gasar Firemiya, da kuma Copa Argentina cikin watanni shida da dawowarsa.

Maradona, mai shekaru 55, ya fito a wasanni sau 70, kuma yayi nasarar zara kwallaye 35 ga kulub din na Boca, tsakanin shekarun 1980 da 1990.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China