Sanarwar ta ce, shugabannin biyu sun bayyana cewa, muddin ana son tabbatar da zaman lafiya cikin dogon lokaci a yankin gabashin kasar Ukraine, da cikakken yankin kasar, akwai bukatar a cimma matsaya guda game da yin gyare-gyare ga tsarin mulkin kasar, da kuma shirya zaben kananan hukumomi a Ukraine.
A ranar 12 ga watan Febrairun bana ne, a birnin Minsk, hedkwatar kasar Belarus, shugabannin Ukraine, Rasha, Jamus, da Faransa suka daddale yarjejeniya game da matakan da za a dauka don warware rikicin Ukraine cikin dogon lokaci, da gaggauta tsagaita bude wuta a yankin gabashin kasar. Yanzu dai an kusan kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa a galiban yankunan gabashin kasar, amma kwanan baya, halin da ake ciki a yankin gabashin kasar ya ci gaba da tsananta, inda aka ci gaba da yin musayar wuta tsakanin sojojin gwamnatin da dakarun da ke adawa da ita.(Bako)