in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Putin ya sa hannu kan kudurin dakatar da yarjejeniyar shige da fice cikin 'yanci tare da Kiev daga ranar daya ga watan Janairu
2015-12-17 10:50:22 cri
Shugaban kasar Rasha Vldimir Putin ya sanya hannu a ranar Laraba kan wani kudurin dakatar da yarjejeniyar shige da fice cikin 'yanci tsakanin Rasha da Ukraine daga ranar daya ga watan Janairun shekarar 2016, ranar da kuma kudurin shige da fice cikin 'yanci tsakanin Kiev tare da kungiyar tarayyar Turai EU zai fara aiki. Bisa tanade tanaden wannan kuduri, Ukraine ba za ta samu gajiya ba bisa sharadin wata kasar da aka fi baiwa fifiko ba bisa tsarin yarjejeniyar musanya cikin 'yanci ta gamayyar kasashe masu 'yanci (CEI), da ma jerin wasu matakan sassauci a fannonin ci-rani, kwastan, kiwon lafiya da zuba jari, in ji ministan cigaban tattalin arzikin kasar Rasha, Alexei Oulioukaiev a gaban 'yan jarida.

A shekarar 2014, Ukraine da kungiyar EU sun rattaba hannu domin kafa wani yankin musanya cikin 'yanci tsakanin bangarorin biyu. Bisa nuna damuwar Moscow, tarayyar Turai ta gusa aiwatar da wannan yarjejeniya har zuwa ranar daya ga watan Janairun shekarar 2016. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China