A gun taro karo na 29 na majalisar hakkin bil'adam ta MDD, an zartas da daftarin kudurin yin hadin gwiwa da ba da agaji a fannin hakkin bil'adam ga Ukraine bisa kuri'u 21 na nuna amincewa, da kuma 6 da rashin nuna amincewa, a yayin da wasu kasashe 20 suka janye jiki daga jefa kuri'ar. Wakilin Sin a yayin taron ya jefa kuri'ar kin amincewa.
Kafin jefa kuri'a, wakilin Sin Ren Yisheng ya yi jawabin cewa, wasu abubuwan dake cikin daftarin sun wuce iznin da majalisar hakkin bil'adam ke da shi, shi ya sa za su tsananta yanayin da ake ciki,da kawo cikas ga yunkurin daidaita batun Ukraine a siyasance.(Fatima)