Gwamnatin kasar Yemen ta zargi dakarun Houthi da rashin girmama yarjejeniyar, inda suka ci gaba da gudanar da aikin soja. Bayan wasu mintuna da sanar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar a ranar Talata, dakarun Houthi sun kai hari a yankuna da dama na jihar Taiz da ke kudancin kasar.
Bugu da kari, dakarun sun kai hari a jihar Marib dake arewacin kasar, inda suka yi yunkurin sake kwace yankin da suka taba mamayewa a baya.
Ko da yake dakarun Houthi sun musunta wannan zargi, suna masu cewa, sojojin hadin gwiwa na kasa da kasa da kasar Saudiyya ke jagoranta sun sha saba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, ganin yadda suka ta kai hare-hare ta sama a jihohi da dama, wadanda suka haddasa mutuwar mutane da dama. (Zainab)