in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aljeriya za ta kara yawan iskar din da take hakowa
2016-01-29 10:42:15 cri

Mahukuntan kasar Aljeriya sun bayyana aniyyarsu ta kara yawan mai da iskar din da suke hakowa, domin biyan bukatun cikin gida da na sauran kasashen duniya.

Firaministan kasar Abdelmalik Sellah wanda ya bayyana hakan, ya kuma yi hasashen karuwar bukatar makamashi mai tsafa a shekarun da ke tafe, ciki kuwa har da iskar gas.

Bayanai na nuna cewa, a shekarar 2015, kamfanin hako iskar gas na Sonatrach ya taimakawa kokarin kasar na kara yawan iskar gas din da ake hakowa a kasar da kashi 2.3 cikin dari.

Firaministan ya ce, duk da haka, dole ne kasar ta kara yawan iskar gas din da ke hakowa, muddin tana son biyan bukatun kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa ta fuskar makamashi.

Sai dai faduwar farashin mai a kasuwannin duniya da kanfon kudaden shiga da kasar ke fuskanta a 'yan watannin nan, ya tilastawa kasar ta Aljeriya sake fadada sassan tattalin arzikin kasar da ya dogara kan mai ta hanyar tsara wasu manufofin raya masana'antu a shekarun da ke tafe.

Yanzu haka gwamnatin kasar ta kebe dala biliyan 90 don inganta fannonin hako iskar gas, duk da raguwar kudaden harajin da take fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China