za a kira taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashen kungiyar G20 na tsawon kwanaki biyu a birnin Shanghai. Kafin a fara taron, mataimakin ministan kudi na kasar Sin Mista Zhu Guangyao ya bayyana a Alhamis din nan cewa tattalin arzikin duniya na fuskantar hadarin koma baya, domin hakan ne kuma ya kamata mambobin kasashen G20, su daidaita manufofinsu na tinkarar wannan matsala, da karawa kasuwanin duniya kwarin gwiwa.
Kaza lika Mista Zhu ya kara da cewa, a matsayin ta na mai saukin taron na wannan karo, Sin za ta sauke nauyin dake wuyanta daga fannoni uku. Na farko za ta yi hadin gwiwa da sauran mambobin G20 don tinkarar kalubalolin da ake fuskanta, na biyu kuwa, za ta kara karfafa G20, da mai da kungiyar wani muhimmin dandali na daidaita batun tattalin arziki, da hada-hadar kudi a duniya. Kana kuwa, za ta sa kaimi ga kasashe mambobin kungiyar wajen ci gaba da hadin gwiwa tsakaninsu, ta yadda za a karawa kasuwannin duniya kwarin gwiwa. (Amina)