in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama da Putin sun cimma matsaya wajen tafiyar da mulkin rikon kwarya a Syria
2015-11-16 09:58:34 cri

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tare da takwaransa na Amurka Barack Obama sun yi tattaunawa yayin taron G20, kuma sun samu fahimatar juna game da batun tafiyar da mulkin rikon kwarya a Syria. A yayin wannan tattaunawa ta mintuna 35, shugabannin biyu sun yi musanyar ra'ayi kan rikicin Syria da Ukraine.

A ranar Asabar, Amurka, Rasha da sauran manyan kasashe na shiyyoyi sun cimma ra'ayi guda kan ajandar kafa wata gwamnatin wucin gadi a Syria, da kuma shirya zabuka cikin wa'adi na watanni 18, ba tare da cimma wata matsaya ba kan makomar shugaban Syria Bashar al-Assad.

Shugaba Putin da shugaba Obama sun cimma ra'ayi guda kan wajabcin ganin wani mulkin rikon kwarya da 'yan Syria za su kai da kansu, da kuma zai fara da tattaunawa tsakanin 'yan adawa da gwamnatin Syria a karkashin jagorancin MDD, da tsagaita bude wuta, in ji wani jami'in White House a gaban manema labarai.

Mai ba da shawara ga shugaba Putin kan harkokin wajen kasar, Yuri Ushakov, ya bayyana a gaban 'yan jarida cewa, Putin da Obama sun tattauna musammun ma kan rikicin Syria, amma kuma sun tabo batun hare haren ta'addanci na Paris. Shugabannin biyu sun cimma matsaya kan makasudan dabaru wajen yaki da kungiyar IS, amma sai dai akwai sabanin ra'ayi kan hanyoyin da za'a bi wajen murkushe matsalar ta'addanci, musamman ma a kasashen Syria da Iraki tsaki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China