Omeruo, dai zai kasance a tare da Kasimpasa ne har zuwa karshen kakar wasannin tun bayan da kulob din sa ya ba da aronsa.
Dan wasan mai shekaru 22, yana fatar zamansa da kulub din na kasar Turkiyya ya kara daga martabarsa domin ya samu damar wasa karkashin kulub din da Sunday Oliseh ke jagoranta.
Omeruo na daga cikin 'yan wasan Chelsea 32, ya shedawa manema labaru cewar, zai iya samun wancan matsayi da yake hari ne idan har ya taka rawar gani a yayin kasancewar sa tare da Kasimpasa.
Ya kara da cewa, raunin daya samu shine ya haifar masa samun matsala da kulub din Super Eagles amma har yanzu yana burin saka komawa don bugawa kasar sa wasa.
Omeruo dai ya buga wasa a Najeriya ne tun da farko a watan Janairun shekarar 2013, kuma ya buga wasan a wannan shekarar ne a wasannin cin kofin kasashen Afrika da na cin kofin duniya a shekarar 2014.(Ahmad Fagam)