Shugaba Xi ya ba da shawarar karfafa yin kirkire-kirkire a matsayin hanyar bunkasa tattalin azrikin duniya
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya ba da shawarar karfafa manufofin tattalin arziki na cikin gida, da bunkasa kirkire-kirkire a matsayin hanyoyin raya tattalin arzikin duniya. Shugaba Xi wanda ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar a zaman farko na taron kolin kungiyar G20 da ke gudana a kasar Turkiya. Ya bayyana cewa, kamata ya yi kungiyar ta G20 ta yi kokarin daidaita ci gaban tattalin arzikin duniya na dan gajeren lokaci kafin a kai ga bullo da sabbin dabarun bunkasar tattalin arzikin na dogon lokaci. Shugaba Xi ya ce, kasar Sin na da tabbaci da karfin dorewar ci gaban tattalin arzikinta na matsakaici zuwa babban mizani, za kuma ta ci gaba da samar wa sauran kasashe damammakin ci gaba. Shugaba Xi ya kara da cewa, an yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar ta Sin zai bunkasa da kimanin kaso 7 cikin 100 a wannan shekara, kuma zai ci gaba da ba da gudummawar a kalla kaso 1 bisa uku ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya. A cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin na fatan karkata ga tsarin kirkire-kirkire, alkinta muhalli, bude kofa ga kasashen waje, da musayar ci gaba. Matakan da a cewar shugaba Xi za su taimaka ga ci gaban tattalin arzikin kasar. Bugu da kari, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kasar Sin za ta kara mayar da hankali wajen inganta rayuwar al'ummar kasar kamar yadda aka tsara a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 13 tare da tabbatar da cewa, kowa ne dan kasa ya ci gajiyar ci gaban da aka samu. (Ibrahim)