in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi da Putin sun jaddada aniyar hada kai da juna a taron G20
2015-11-16 09:43:13 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa Vladimir Putin na Rasha, sun gana a Lahadin nan tare da yin alkawarin ci gaba da karfafa dangantakar dake tsakanin su domin amfanin kasashen biyu.

Shugaba Xi, ya shedawa mista Putin cewar, kasar Sin za ta samar da wani tsarin kasuwanci na bai daya, wanda zai hade illahirin mambobin kasashen 20 mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Ana sa ran kasar Sin ne za ta karbi bakuncin taron na G20 a shekara mai zuwa, shugaba Xi Jinping ya ce, za su hada gwiwa da Rasha wajen gudanar da shirye shiryen karbar bakuncin taron, kuma ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa tsakanin su bayan gudanar da taron na G20 karo na 10 a birnin Antalya na kasar Turkiyya.

A nasa bangaren, shugaba Putin ya ce, Rasha za ta marawa kasar Sin baya a yunkurin ta na karbar bakuncin taron a badi, wanda ake sa ran zai aza harsashen tabbatar da hadin kan kasashen masu karfin tattalin arziki a duniya.

Shugabannin biyu, sun yi alkawarin karfafa hadin kai a tsakanin su bisa tsarin jadawalin da kasashen BRICS ke amfani da shi a halin yanzu, a bangarorin tattalin arziki da siyasa da musayar kudi da makamashi da kuma raya al'adu.

Putin ya tabbatarwa shugaba Xi cewar, manufar kasashen Rasha da Sin guda ce wajen tabbatar da yin biyayya sau da kafa ga dokokin kasa da kasa a yayin gudanar da al'amurran da suka shafi hulda ta kasa da kasa, yayin da shugaba Xi ya bayyana fatar kasashen biyu za su ci gaba da hada gwiwa domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China