A yayin ganawar, shugaban kasar Sin mista Xi Jinping ya yi wani jawabi mai taken 'samar da karin damammaki da tinkarar kalubale', inda ya gabatar da shawararsa kan yadda za a sanya kasashen BRICS su kara taka muhimmiyar rawa a fannin al'amuran kasa da kasa. Shawarar shugaban ita ce, da farko, a samar da wani yanayi da zai taimakawa kokarin da ake na samar da ci gaba, da kyautata tsarin tattalin arzikin duniya. A cewarsa kamata ya yi a sanya bangarorin duniya su lura da cewa kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa sun samar da kashi 50 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin duniya, lamarin da ke nuna cewa, suna samar da gudunmawa sosai ga kokarin raya tattalin arzikin kasashe daban daban.
Na biyu shi ne, kasashe mambobin BRICS su kara taimakawa juna don tinkarar kalubalolin da ake fuskanta a duniya. A cewar shugaban, hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Paris sun nuna bukatar dake akwai ta kara yin hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban don dakile ta'addanci, ya kamata a bi ka'idojin MDD, gami da kokarin kau da matsalar daga tushe.
Na uku, in ji shugaban kasar Sin, shi ne kara azama ga kokarin hadin kai tsakanin bangarorin duniya don amfanawa junansu. Ya kamata kasashe masu tasowa su yi kokarin sa kaimi ga kasashe masu sukuni don su cika alkawuran da suka dauka, ta yadda za a karfafa huldar da ta dace tsakanin kasa da kasa, wadda za ta kula da bangarori daban daban, tare da samar da ci gaba a duk duniya.
Sa'an nan na hudu kuma na karshe shi ne, kokarin hadin kai da kasashe daban daban don kyautata tsarin tattalin arziki, tare da samar da kasuwannin da za su tabbatar da moriya ga kowa. A cewar shugaban kasar Sin, kasar Sin na son cin gajiyar damammakin ci gaban da ta samu tare da sauran mambobin BRICS, da kara yaukaka huldar hadin gwiwa tsakanin su, musamman ma a fannin tattalin arziki.(Bello Wang)