Har ila yau mujallar ta bayyana cewa kamfanoni guda 89, na babban yankin kasar Sin ne da kuma HongKong, inda kuma saura 6 suke daga yankin Taiwan. Kamfanonin Amurka guda 132 ne suka shiga jerin wannan adadi, wanda hakan ya yi daidai da na shekarar bara.
Bugu da kari, cikin wannan shekarar da muke ciki, an daga mizanin yawan kudin da kamfanonin zasu mallaka kafin shigarsu wannan jadawali da dallar Amurka biliyan 1.2, inda yanzu sabon adadin ya kai dallar Amurka biliyan 23.2. Sa'an nan kuma, binciken mujallar ya nuna cewa gaba daya, wadannan kamfanoni sun samu kudin shiga da yawansa ya kai dallar Amurka biliyan dubu 30.3, adadin ya karu da kashi 2.77 bisa dari, idan ana kwatanta da abinda aka samu a bara. Amma moriyar da wadannan kamfanoni guda 500 suka cimma a shekarar ta bana, ya ragu da dallar Amurka biliyan 100, lamarin ya nuna koma baya ta fuskar yanayin tattalin arzikin duniya da ake ciki. (Maryam)