in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da bikin baje koli na Sin da Afrika a Habasha
2015-11-13 10:07:28 cri

An kaddamar da bikin baje kolin kayayyaki da fasahar zamani da aikin hidima na kasashen Afrika da Sin na shekarar 2015 a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Bikin wanda za'a shafe tsawon kwanaki 3 ana gudanarwa, daga ranar 12 zuwa 14 ga wannan watan, kuma ya zo daidai da shirin kasuwancin hadin gwiwa na Sin da kasar Habasha, wanda ke da manufar karfafa dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afrika.

Sama da fitattun kamfanonin 100 daga kasar Sin ne suka halarci bikin, wanda aka shirya da nufin karfafa huldar kasuwanci tsakanin kasar Sin da Habasha da sauran kasashen Afrika.

Da yake gabatar da jawabi a yayin taron, mataimakin ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin, Qian Keming, ya ce, taron na da matukar muhimmanci wajen karfafa dangantaka da huldar kasuwanci a tsakanin 'yan kasuwar kasar Sin da sauran kasashen nahiyar Afrika.

Qian Keming, ya ce, taron, zai ba da dama ga bangarorin biyu su tattauna hanyoyin da za su karfafa huldar dangantaka da cimma yarjejeniya tsakanin su.

Bugu da kari a ranar Alhamis din, kasar Sin da Habasha suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar, inda kasar Sin za ta samar da kudin Renminbi yuan miliyan 50 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 7.93 domin tallafawa kasar don samar da agajin abinci.

Mataimakin ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin Qian Keming da takwaransa ministan kudi da tattalin arziki na kasar Habasha Abdulaziz Mohammed, sun sanya hannu kan yarjejejniyar a birnin Addis Ababa.

Kasar Sin ta samar da tallafin ne, ga wadanda matsalar fari ta shafa a kasar ta gabashin Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China