in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka sun kafa ofishin shiga tsakani domin warware matsalolin cinikayya da kwadago
2015-11-27 09:13:13 cri

Manyan lauyoyi daga kasar Sin da na wasu kasashen Afirka, sun kaddamar da wani sabon ofishi na sauraro, da warware takaddamar cinikayya da ta kwadago tsakanin sassan biyu.

Rahotanni sun ce, ofishin na CAJAC wanda aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, zai rika warware matsalolin kasuwanci a fannoni daban daban, a wani mataki na kaucewa shigar da kararraki gaban kotu.

Yanzu haka dai an nada masanin shari'a Michael Kuper 'dan kasar Afirka ta Kudu a matsayin shugaban ofishin na farko.

Bude ofishin na CAJAC ya zo daidai gabar da hada hadar cinikayya tsakanin Sin da nahiyar Afirka ke dada bunkasa.

Da yake karin haske game da muhimmancin bude ofishin, Mr. Kuper ya ce, CAJAC zai tabbatar da gaggauta sauraro, da magance korafe-korafe game da sabani daka iya aukuwa tsakanin 'yan kwadago, da 'yan kasuwa dama wasu sassan na gwamnatocin Sin da Afirka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China