in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sanda a Kenya na bincikar zargin ta'ammali da kwaya a fagen wasanni
2016-02-17 09:15:55 cri
Jami'an tsaro a kasar Kenya su kaddamar da wani bincike game da zargin laifin ta'ammali da muggan kwayoyi a tsakanin 'yan wasan kasar, inda suka bayyana laifukan a matsayin abubuwn dake zubarwa kasar wacce ke gabashin Afrika mutunci a idon duniya.

Wannan yunkuri ya zone bayan da hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya WADA ta ce ta mika batun zargin yin ta'ammali da haramtattun kwayoyin a kasar Kenya ga sashen hukumar mai bin diddigi, bayan da kasar ta gaza shawo kan wannnan muguwar dabi'a.

Sifeto janar na hukumar yan sandan kasar Joseph Boinnet, ya tabbatar a ranar Lahadin data gabata cewar, dama tuntuni jami'an 'yansandan kasar suka dukufa wajen zakule mutanen da ake zargi, kuma nan bada jimawa ba zata damke dukkan mutanen dake da hannu a zargin ta'ammali da muggan kwayoyin.

Boinnet ya ce, mutanen dake aikata laifukan shan miyagun kwayoyin a tsakanin 'yan wasan kasar ta Kenya, suna matukar zubar da kimar harkar wasanni kasar.

Rahotanni sun bayyana cewar, mai yiwuwa ne WADA ta sanyawa Kenyar takunkumi kamar yadda aka azawa kasar Rasha, to sai dai hukumar mai yaki da ta'ammali da miyagun kwayoyin ta kasa da kasa ta fada a Juma'ar data gabata cewar, wannan rahoto bashi da inganci, kasancewar har yanzu batun na gaban kwamiti bin diddigi.

WADA zata kammala bibiyar wannan batu, idan har ta gamsu cewer yan wasan tseren kasar su 40 an same su dumu dumu da hannu wajen aikata wannan laifi na ta'ammali da harantattun kwayoyi, kasar ta Kenya zata iya fuskantar hukuncin haramta mata shiga gasar wasannin hunturu na kasar Brazil.

WADA, ta tabbatar da cewar an samu ci gaba game da ayyukan hukumar na binciken ta'ammali da haramtattun kwayoyin, sai har yanzu akwai jan aiki a gaban hukumar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China