Yanzu haka dai saura kasa da watanni 6 a bude gasar birnin na Rio. Kafin kammalar nune nunen da suka gabata, 'yan wasannin motsa jiki na da dana yanzu, sun bi sahun masu sha'awar wasanni wajen gudanar da bukukuwa da dama a Sambodromo, garin da ya karbi bakuncin nune nunen na birnin Rio.
Da take bayyana farin cikin ta ga gudanar bikin, shahararriyar 'yar wasan kwallon raga ta mata a kasar Brazil Gabi Guimaraes, ta ce kowa na cikin nishadi saboda karatowar wannan babbar gasa dake tafe cikin watan Agustan bana, lokacin da birnin Rio zai karbi bakuncin gasar Olympic ta farko da zata gudana a nahiyar kudancin Amurka.
Tuni dai shahararriyar makarantar horos da 'yan kwallo ta samba dake kasar Brazil, ta shirya kasaitaccen bikin raye-raye a ranar 7 ga watan nan na Fabarairu, wato ranar farko ta gudanar shagulgulan da suka gabata. Cikin na ta tsarin, makarantar ta Samba ta shirya gasar raye raye, ciki hadda ma gargajiyar al'ummar Girka, da kuma wasu wasannin motsa jiki da suka kunshi tseren kekuna, da wasan alkafura ta guragu.
Dan wasan tseren yada kanin wani, wanda ya zamo na uku a gasar tseren birnin Athens cikin shekarar 2014, Vanderlei Cordeira de Lima, duk kuwa da harin da aka kaddamar a yayin tseren, a wannan karo shi ne ya jagoranci masu nune nunen wasannin da Samba ta shirya, inda ya wuce gaba dauke da fitila, makamanciyar wadda za a yi amfani da ita a yayin gasar Olympic ta birnin Rio dake tafe.
Rahotanni na cewa da zarar an gama shagulgulan nuna wasannin da ake yi, birnin Rio zai shirya wasannin gwaji har guda 22, domin kara share fagen gasar da ake dako.(Saminu Alhassan)