in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulub din CSKA na Rasha bazai sayar da dan wasa mai tsaron bayansa Ahmed Musa a matsayin musaya ba
2016-02-04 16:36:43 cri
Kulub din CSKA na kasar Rasha ya soke tallar neman samun dan wasan sa a karo na 4 daga kulub din Leicester City a kan dala miliyan 26 da rabi tun a makon jiya, wanda hakan wani ci gaba ne da aka samu sama da farashin farko da aka ambata na dala miliyan 21 da digo 6.

Dan wasan mai shekaru 23 an yi amanna cewar, zai iya yarda sauya shekarsa zuwa tsarin wasannin Premier League na kasar Birtaniya.

Sai dai kuma, CSKA, wanda shi ne babban kulob din wasannin Premier ta kasar Rasha yana so a jinkirta wannan yunkurin har zuwa lokacin zafin bana.

Musa ya sake daukar hankalin manyan kuloflikan tsarin gasar Premier League na Birtaniya ,wanda aka kayyade cikin kwantiragin zuwa shekarar 2019 cewa, ba za a sami dan wasan ba kafin an biya dala miliyan 32 da rabi ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China