in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin babbar kawa ce ta Zimbabwe, in ji kusoshin kasar ta Zimbabwe
2015-11-29 17:52:29 cri
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe da kuma ministocin gwamnatin kasar da dama sun bayyana a kwanakin cewa, suna Alla-alla da ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping da zai kai a kasar, kuma suna ganin cewa, ziyarar za ta kara inganta huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Mugabe ya ce, Sin babbar kawa ce ta Zimbabwe a duniya, kuma ziyarar da shugaba Xi Jinping zai kai kasarsa zai kasance wani muhimmin al'amari ga ci gaban huldar kasashen biyu, inda ake sa ran bangarorin biyu za su tattauna batutuwan hadin gwiwa da ke shafar fannoni da dama a tsakaninsu, kuma ana fatan Sin za ta taimaka wa Zimbabwe din wajen aiwatar da wasu muhimman shirye-shiryen da ke nasaba da tattalin arziki da ma zaman rayuwar al'umma , tare kuma da gaggauta bunkasuwar tattalin arzikin wannan kasa

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China