in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa Oliseh ya fuskanci matsala da hukumar NFF
2016-02-03 15:30:57 cri
Rahotanni daga hukumar gudanarwar kwallon kafar Najeriya NFF, na nuna yadda wasu ke hasashen cewa kocin kungiyar kwallon kafar kasar Super Eagles wato Sunday Oliseh, na iya fuskantar matsala sakamakon kalaman da suka rika fitowa daga bakin sa a kwanan nan. Hakan dai na zuwa ne bayan da aka fitar da kungiyar Super Eagles daga gasar cin kofin kasashen Afirka, wadda hukumar CHAN ke gudanarwa a kasar Rwanda.

Shi dai Oliseh ya rika zargin masu ruwa da tsaki a harkar wasannin kasar da gaza sauke nauyin dake wuyan su na karfafa gwiwar kungiyar, har ma ta kai yana cewa ya kashe kudi daga aljihun sa, har dalar Amurka 4000 lokacin da 'yan wasan na Najeriya ke atisaye a birnin Pretoria na Afirka ta kudu, gabanin fara buga wasa a gasar ta kasar Rwanda.

Game da hakan, wani jami'in hukumar NFF da ya nemi a boye sunan sa, ya bayyana cewa suna sane da irin kalaman da Koci Oliseh ke yi a kafafaen radio da jaridu, kuma zasu dauki matakin da ya dace a kan sa a lokaci mafi dacewa.

Jami'in ya ce kamata yayi Oliseh ya karbi alhakin gazawar sa, ya kuma fara shirin tinkarar wasannin share fagen gasar AFCON da kungiyar sa za ta buga da kasar Masar, amma maimakon haka ya zabi ya dorawa hukumar NFF laifi. Ya ce halayyar da kocin ke nunawa ta sabawa ka'idojin ayyukan hukumar, duk kuwa da cewa ya san hakan, duba da cewa an bashi kwafin ka'idojin aiki, kafin ya fara aiki da a matsayin kocin na Super Eagles.

Wasu dai sun fara hasashen cewa mai yiwuwa ne hukumar ta NFF ta dakatar da Oliseh ko rage masa mukami daga babban mai horas da 'yan wasan na Super Eagles, idan har aka tabbatar da laifin da ake zargin sa da aikatawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China