A yayin da majalisar ke gudanar da zamanta a ranar Litinin din nan a helkwatar majaisar dokokin dake Tubrug, kimanin 'yan majalisar 89 daga cikin mambobi 104 ne suka kada kuri'ar kin amincewa da bukatar kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasar.
'Yan majalisun dai, sun bayyana cewar, gwamnatin kasar wacce majalisar kolinta ke zaune a Tunisiya ta tara mukamai masu yawan gaske, kuma ana sa ran nan da kwanaki 10 masu zuwa ne za ta gabatar da wani karamin kaso daga cikin sabbin sunayen ministocin kasar.
A ranar 19 ga watan Janairu majalisar zartaswar dake zaune a Tunisiya, wacce aka kafa ta karkashin yarjejeniyar MDD, ta sanar da aniyar kafa gwamnatin hadin kan kasar wadda za ta kunshi ministoci 32 da kuma mataimakan Firaiminista 4. (Ahamd Fagam)