An gudanar da wadannan tattaunawa ne bayan da majalisar wakilai mai matsuguni a Tobruk wadda kasashen duniya suka amince da ita ta yi watsi da majalisar zartarwar da ta gabata.
Bisa ga yarjejeniyar da wakilan bangarorin Libya a tattaunawar suka sanyawa hannu a watan Disamba, an amince sabuwar gwamnatin da kasance a birnin Tripoli, ta kuma samu amincewar majalisar dokokin kasar.
Jami'an kasar Morocco sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, ana gudanar da tattaunawar kafa sabuwar gwamnatin mai mukamai da dama ne a asirce.
Majalisar zartarwar da ke da matsuguni a Tunisiya na da kwanaki 10 daga yanzu domin ta gabatar da sunayen sabbin ministoci.(Ibrahim)