Gwamnatin kasar Afirka ta kudu ta bayyana cewa, bayan da aka aiwatar da sabuwar manufar, yawan hasarar da aka samu a wasu wuraren yawon shakatawa kamar a Dutsen Tebur na kasar ya riga ya kai dalar Amurka miliyan 540.
Sakamakon haka, ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar ta tsai da kudurin yin kwaskwarima kan manufar neman izinin shiga kasar bisa matakai 3, wato, a cikin watanni 3 masu zuwa, masu yawon shakatawa na kasashen waje za su iya gabatar da takardun neman izinin shiga kasar Afirka ta kudu ta hanyar aike da takardunsu zuwa ofisoshin jakadancin kasar dake kasashen duniya ta gidajen waya maimakon zuwa da kansu. Sannan a cikin shekara daya mai zuwa, mai yiyuwa ne kasar Afirka ta kudu za ta yarda da masu yawon shakatawa na kasashen BRICS, kamar na Sin da Rasha da Indiya da su ziyarci kasar Afirka ta kudu ba tare da izini ba.
Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar Afirka ta kudu ta jaddada cewa, wadannan sabbin manufofi za su iya samun daidaito tsakanin batun tsaron kasar da moriyar tattalin arzikin kasar, amma ba za su kawo barazana ga yara ba. (Sanusi Chen)