in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: Za a jinkirta zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar CAR
2015-12-25 09:35:38 cri
Rahotanni daga Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na cewa, za a jinkirta zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin kasar da tsawon kwanaki uku, ta yadda za a samu damar horar da malaman zabe da warware wasu matsalolin da suka shafi gudanar da zaben kansa.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ne ya bayyana hakan ga taron manema labarai. Yana mai cewa hukumar zaben kasar ce ta sanar da hakan a jiya Alhamis.

Dujarric ya shaidawa taron manema labaran cewa, tun a jiya Alhamis kayayyakin zaben suka iso Bangui, babban birnin kasar kuma nan ba da dadewa ba tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD da ke kasar wato MINUSMA za ta fara raba kayayyakin zuwa sauran lardunan kasar.

A baya dai an shirya gudanar da zabukan ne a ranar Lahadi 27 ga wata, amma yanzu aka kara jinkirta zabukan da kwanaki uku.

Ana fatan zabukan su maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ,tun bayan da 'yan tawayen Seleka galibin su muslumi suka kwace mulki a kasar galibin al'ummarta kiristoci a shekara 2015, lamarin da ya haifar da mayar da martanin kana daga bisani ya rikide zuwa fadan kashe-kashen addini.

A wani labarin kuma, jami'in na MDD ya bayyana cewa, ana ci gaba da kwance damarar makamai da shirin sulhuntawa a kasar. Ya ce, yanzu haka 'yan tawayen Seleka da na Anti Balaka da ke yankin Kaga Bandoro sun mika makamai 35 da albarusai sama da 100 da ke hannunsu.

Sannan a karon farko a yankin Bouar, wasu mayakan Anti Balaka guda 70 sun mikawa sojojin makaman da ke hannunsu bisa radin kansu

Sakamakon tashin hankalin da ya yi kamari a kasar ne ya tilastawa shugabar rikon kwaryar kasar Catherine Samba-Panza dage zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 18 ga watan Oktoba.

Bayanai na cewa, al'amura sun dan lafa a kasar tun bayan da aka kara tura dakarun MDD da na kungiyar AU zuwa kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China