Tawagar wucin gadin wanda za'a tura sakamakon gayyatar da gwamnatin kasar ta yi za ta isa birnin Bangui ne a ranar 20 ga wata kuma za ta kasasnce a cikin kasar har zuwa 30 ga wata, a bayanin da kungiyar AU ta fitar a jiya Jumma'a.
Tawagar sa ido a zabe na kungiyar AU zai kasance karkashin jagorancin Souleymane Ndene Ndiaye, tsohon Firaministan kasar Saliyo inji sanarwar.
Za'a tura jami'an sa idon a dukkan gundumomin zaben kasar domin lura da yadda za'a tafiyar da zaben da kuma tattaunawa da manyan masu ruwa da tsaki a cikin ayyukan zaben inji sanarwar AUn. (Fatimah)