Cikin 'yan makwannin baya bayan nan, shirin samar da abinci na MDD da abokan aikinsa, sun kara fadada ayyukan tallafi da suke baiwa fararen hula, wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a kasashen Chadi da Kamaru.
A cewar kakakin MDD Farhan Haq, a kasar Chadi kadai, sama da mutane 5,000 da suka rasa matsugunnan su ne suka samu tallafin abinci mai gina jiki a karon farko, tun bayan da yanayin tsaro ya dakile hanyar taimaka musu.
Mr. Haq ya ce, ana ci gaba da gudanar da wannan aiki, inda cikin wannan wata na Fabrairu, ake fatan kara agazawa wasu karin mutane 35,000 dake matukar bukatar tallafi.
Ofishin WFP dai ya bayyana cewa, sama da mutane miliyan 5 da dubu dari 6 ne rikicin Boko Haram ya jefa cikin yanayi na kamfar abinci a Najeriya, da Kamaru da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar.
Rahotanni na nuna cewa daga shekarar 2013, lokacin da kungiyar ta fara kaddamar da hare hare a Kamaru, kawo wannan lokaci mutane kimanin 1,000 ne rikicin ya hallaka.
Wata sanarwa da aka fitar a jiya Litinin, ta rawaito ministan sadarwar kasar Kamarun Issa Tchiroma Bakary, na cewa 'yan Boko Haram sun kaddamar da hare hare har 315, da suka kunshi harin kunan bakin wake 32, da na binne ababen fashewa 12, a yankin arewa mai nisa dake kasar ta Kamaru.
A daya hannun, ofishin OCHA mai kula da ayyukan jin kai, ya ce baya ga rasa rayuka, ayyukan kungiyar Boko Haram ya kuma raba kimanin mutane 100,000 dake zaune a yankin tafkin Chadi da muhallin su.(Saminu Alhassan)