in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani harin kunar bakin wake ya halaka mutane kusan 60 a Najeriya
2016-02-11 12:15:11 cri
Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 60 ne suka gamu da ajalinsu kana 78 suka jikkata, sakamakon wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a sansanin 'yan gudun hijira na garin Dikwa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Borno Satomi Ahmad, ya bayyana cewa, wasu mata 'yan kunar bakin wake guda biyu ne suka shiga sansani kana suka tayar da bam din da ke jikinsu a lokacin da 'yan gudun hijirar ke layin karbar abinci.

Hukumar ta sanar da cewa, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke yankin.

Sai dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma mazauna sansanin na zargin kungiyar Boko Haram da kaddamar da wannan harin, inda a halin yanzu ta fadada hare-haren da ta ke kaiwa zuwa yankuna tafkin Chadi. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China