in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An zargi wasu lauyoyi da 'yan jarida da laifin dakile yaki da cin hanci
2016-02-17 10:04:27 cri

Shugaban hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa Ibrahim Magu, ya zargi wani sashi na lauyoyi da 'yan jaridar kasar da lafin yunkurin dakile nasarar ayyukan hukumarsa.

Magu ya bayyana hakan ne ga gamayyar kungiyoyin fararen hula na kasar wato CSO, yayin wani tattaki da wakilan su suka yi zuwa ofishin hukumar dake birnin Abuja, inda suka tabbatar da goyan bayan su ga ayyukan hukumar.

Jagoran na EFCC ya kara da cewa, manyan lauyoyin kan gabatar da bukatu masu sarkakiya ga kotuna, domin hana hukunta wadanda suka sace kudin kasa, bayan da irin wadannan lauyoyi suka cika aljifan su da kudin haram.

Magu ya ce, abun bakin ciki ne matuka, ganin yadda irin wadannan lauyoyi ke yiwa kasar da ta yi musu halasci kafar ungulu, musamman duba da yadda suka yi matukar amfana daga Najeriya ta fuskar daukar nauyin karatun su. Amma sai ga shi a cewar sa irin wadannan lauyoyi ne a yanzu, ke kare masu muggan laifukan wawashe kudaden da ya dace a yi amfani da su wajen gina asibitoci, da samar da magunguna, da ma kayan da ake bukata wajen yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda kamar Boko Haram.

Kaza lika Magu ya zargi wasu 'yan jaridu da ake amfani da su wajen bata sunan hukumar, suna zargin ta da kin martaba dokokin kasa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China