Mohammed Usaman, mataimakin shugaban kwamitin kiwon lafiya a zauren wakilan jama'ar Najeriya ya yi wannan furuci a yayin wani taron manema labarai da ma'aikatar kiwon lafiya ta tarraya ta shira domin bikin ranar yaki da ciwon kansa ta duniya ta shekarar 2016 a birnin Abuja, hedkwatar Najeriya.
A nata bangare, madam Ramatu Hassan, babbar jami'ar dake kula da tsarin yaki da cutar kansa a ma'aikatar kiwon lafiya ta tarayya, ta bayyana cewa gwamnati za ta bude cibiyoyin kula da kansa guda bakwai zuwa ga cibiyoyin da suka shahara.
Haka kuma, gwamnati za ta shiga cikin hadin gwiwa na gwamnati da masu zaman kansu (PPP) tare da wasu kamfanoni domin kara yawan cibiyoyin bada kulawa zuwa goma sha hudu a shekaru biyu masu zuwa, in ji madam Ramatu Hassan a gaban 'yan jarida. (Maman Ada)