Kakakin hukumar tsaron farin kaya wato DSS a takaice Tony Opuiyo, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai, ya ce an kama wanda ake zargin ne mai suna Abdussalam Enesi Yunusa bisa wasu bayanan asiri da ke nuna cewa, yana kokarin daukar matasa domin shiga kungiyar ta IS.
Bugu da kari, hukumar ta ce Yunusa ya kammala shirye-shiryen yin tattaki zuwa cibiyar samun horon kungiyar ta IS da ke kasar Libya tare da wasu 'yan Najeriya da ya dauka a matsayin 'ya'yan kungiyar kafin 'yan sanda su kama shi.
Kakakin hukumar ta DSS ya kara da cewa, Yunusa ya shaida musu cewa, yanzu haka akwai wasu matasa guda biyu Ibrahim da Abubakar Ligali da ke samun horo a sansanin kungiyar ta IS da ke kasar Libya.
Bayanai na nuna cewa, shi dai Yunusa, dalibi ne a jami'ar kimmiya ta tarayya da ke Minna a jihar Neja, inda yake karantun digirinsa na farko a fannin ilimin fasahar sadarwa ta zamani. (Ibrahim Yaya)