in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta ce tana mai da hankali a kan ciniki cikin 'yanci
2016-02-16 10:05:11 cri
Najeriya tace zata maida hankali akan ciniki tsakanin kasa da kasa cikin 'yanci duk da yanayin tattalin arzikin da take ciki a yanzu. Shugaban kasar Muhammadu Buhari wanda ya fadi hakan a ganawar da yayi da babban daraktan kungiyar ciniki ta duniya WTO Roberto Azevedo a Abuja ranar litinin din nan, yace kasar zata cigaba da kasancewa a cikin kasuwannin duniya duk da tangaltangal na farashin mai da take fuskanta.

Yace yayi muranan cewa kungiyar WTO tana sane da matsayin da kasar ta samu kanta a ciki, yanayin tattalin arzikin ta da kuma tsarin kayyakain da take saye da ma sauran su.

Duk da hakan in ji shi kasar zata cigaba da maida hankali ma muradin ciniki 'cikin 'yanci na kasa da kasa da kungiyar take himma akai.

Tun da farko Shugaban kungiyar ta WTO ya bayyana farin cikin shi na cewar Najeriya zata cigaba da aiki da manyan hukumomi na kasa da kasa, yana mai cewa kungiyoyin ciniki bada dadewa ba zasu fara tattauna muhimman batutuwa ma kasar.

Yace batutuwa sun hada da cigaban kanana da matsakaitan masana'antu wanda ya bayyana a matsayin samar da mafi yawan guraben aikin yi a kasashe masu tasowa.

Mr Roberto Azevedo daga nan sai ya ce kungiyar WTO na son jawo kamfanoni masu zaman kansu kusa ta yadda zasu iya fahimtar ainihin kalubalen da ake fuskantar, sannan kuma Najeriya tana da babbar rawar da zata taka a ciki duk da wani yanayi mai wahala a fannin tattalin arziki.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China