Maharan, da ke kan babura, sun kashe ba ji ba gani mazauna kauyen Kwanar Dutse dake karamar hukumar Maru, in ji wani jami'in karamar wannan hukuma, Salisu Dangulbi. "Wani lokaci na tashin hankali matuka da ya kuma kwashe tsawon lokaci. Maharan sun yi abin da suka ga dama a tsawon fiye da sa'o'i biyu, tare da kashe da sace al'ummarmu," in ji mista Salisu Dangulbi.
Sanusi Amiru, kakakin 'yan sandan jihar Zamfara, ya bayyana cewa 'yan sanda da aka tura wurin domin mai da doka da oda sun gano gawawwaki kusan goma. "Muna bincike kan wannan hari kuma nuna fatan sanya hannu kan wadanda suka aikata shi", in ji mista Sanusi Amiru.
Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin wannan hari, amma tuni ake danganta shi a kungiyar Boko Haram, dake gudanar da ayyukan ta'addancinta a arewacin Najeriya da yankin tafkin Chadi. (Maman Ada)