Gwamnatin Najeriya ta sallami shugabanin kafofin watsa labaranta guda shida da dake karkashin ma'aikatar watsa labarai da al'adun kasar.
Ministan watsa labarai da al'adu Lai Mohammed shi ne ya bayyana hakan a Abuja, fadar mulkin kasar yayin wata ganawa da shugabannin gidan Talabijin na kasa NTA, gidan rediyon tarayya na Najeriya(FRCN) da muryar Najeriya(VON) da kamfanin dillancin labarai na Najeriya(NAN) da hukumar kula da harkokin watsa labarai(NBC) da hukumar wayar da kan jama'a ta kasa(NOA).
Ministan ya kuma umarci shugabannin da aka sallama da su mika ragamar tafiyar da hukumomin nasu ga manyan jami'an gwamnati da ke wadannan ma'aikatu.
Ya kuma gode musu bisa ga ayyukan da suka yi wa kasa, sannan ya yi musu fatan alheri.(Ibrahim Yaya)