in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manchester City ta tabbatar cewa Pep Guardiola zai karbi matsayin Manuel Pellegrini
2016-02-03 11:19:51 cri

Kulub din Manchester City ya sanar a hukumance cewar Guardiola zai karbi ragamar aiki na shekaru 3 yayin da ake saran Pellegrini zai aje aiki a ranar 30 ga watan Yuni.

Shahararren mai horar da 'yan wasa mai shekaru 45 ya sanar da wannan mataki ne tun a watan Disamba, cewar a halin da ake ciki zai bar kulub din Bayern Munich daga watan Mayu domin ya samu damar zama koci a Ingila a kakar wasanni dake tafe a nan gaba.

Sanarwar da kulub din ya fitar ta ce, Manchester City ya tabbatar da cewar a 'yan makonnin nan ya kammala tsarawa tare da cimma matsaya game da kulla kwantiragi da Pep Guardiola domin ya jagoranci kulub din na MCFC a matsayin mai horas da 'yan wasa a kakar wasanni ta 2016/17. Sa'an nan wa'adin kwantiragin shi ne tsawon shekaru uku.

An dai soma tattaunawa kan wannan yarjejeniyar ne wacce ta taba gamuwa da cikas tun a shekarar 2012. Kulub din yana fatar wannan sauyin na Manuel Pellegrini zai kawo sauye sauye. Manuel, ya goyi bayan wannan mataki dari bisa dari, kuma yayi fatar kwalliya zata biya kudin sabulu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China