Ministan yawon shakawa na kasar Henrique Eduardo Alves, shine ya tabbatar da hakan a lokacin da yake jawabai a taron bajakoli kan harkar yawon bude ido na kasa da kasa a Madrid, ya kara da cewar kimanin dalar Amurka biliyan 11 ne kasar Brazil ta ware don karbar bakuncin gasar ta Rio 2016, kuma ana saran matakin zai janyo hankalin masu yawon bude ido zuwa kasar.
A cewar Alves, kusan kashi 15 cikin 100 na kudaden, an kashesu ne wajen inganta harkokin wasannin, sannan ragowar kason an zuba su ne wajen inganta fasalin birnin domin ya kasance abin koyi.
Ya kara da cewar, sannu a hankali kasar Brazil tana samun bunkasuwa a fannin yawon bude ido, kuma za'a ci gaba da inganta wannan sashen.
A halin yanzu, Brazil ta samu masu yawon bude ido na cikin gida kimanin miliyan 70 da kuma mutane miliyan 6 daga kasashen waje. Saidai Alves yace adadin yayi kadan kasancewar iri guda ne dana Eiffel Tower."
Domin kara adadin baki 'yan kasashen waje zuwa kasar, gwamnatin Brazil, ta dage takunkumin data aza ga masu neman shiga kasar daga kasashen Amurka, da Canada, da Australia da kuma Japan a lokacin gudanar da gasar wasannin ta Olympic, wacce ake fatar zata kara kashi samar da 20 cikin 100 na baki 'yan kasashen waje 'yan yawon bude ido zuwa kasar a cikin wannan shekara.
Bugu da kari, Brazil tana gudanar da Kamfe a shafukan sada zumunta a fadin nahiyar Latin Amurka.
Daga karshe, Alves ya ce babbar matsalar daka iya addabar kasar itace tsaro, a don haka kasar ta zama abin koyi yayin da ta tanadi jami'an tsaro kimanin dubu 80 domin sa ido game da gasar wasannin ta Olympics.(Ahmad Fagam)