Sanarwar ta bayyana cewa, mambobin kwamitin sulhun sun yi fatan wannan mataki zai zamo mai muhimmanci bayan daddale yarjejeniyar siyasar kasar ta Libya. Kwamitin sulhun ya kuma jinjinawa matakin aiwatar da yarjejeniyar a dukkan fannoni, tare da fatan za a amince da sabuwar gwamnatin kasar cikin hanzari, don baiwa gwamnatin damar fara warware matsalolin siyasa, da na tattalin arziki, da ta'addanci a kasar. Kaza lika sanarwar ta jaddada cewa, ya kamata a kafa sabuwar gwamnatin a birnin Tripoli.
A ranar Talata ne kwaminitin firaministan kasar Libya ya sanar da kafa gwamnatin hadin kan al'ummar kasar a hukunce, domin kawo karshen rikice-rikice a kasar. Kwamitin ya gabatar da jerin sunayen ministoci 32 a sabuwar gwamnatin, ciki hadda Faizi Sarraj wanda aka nada firaminsitan kasar. (Zainab)