in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mambobin MDD sun bukaci a sanya takunkumi kan Koriya ta arewa kan shirinta na makami mai linzami
2016-02-08 13:52:26 cri
Kasashen Japan da Koriya ta kudu da kuma Amurka a ranar Lahadin nan bayan wani taron gaggawa na kwamitin tsaron MDD, sun bukaci a sanyawa Koriya ta arewa karin takunkumi, bayan aiwatar da gwajin makaminta mai linzami wanda suke ganin ya keta hurumin dokar MDD.

A wata sanarwar bayan taro, wanda jakada Rafael Ramirez na Venezuela ya karanto, ya ce taron kwamitin mai wakilan kasashe 15, ya yi allah wadai da gwajin makamin da Koriya ta arewa ta gudanar, wanda kasar ta sha yin ikirarin gudanar da gwaji ne domin bunkasa ci gaban fasaharta.

Koriya ta arewar ta sha nanata yunkurin mutunta sabbin dokokin MDD, duk da cewar ba ta aiwatar da su ba kamar yadda ta yi alkawari tun a watan da ya gabata, da ma dai Koriyar tana fuskantar wasu takunkumin da aka aza mata game da rashin aiwatar da yarjejeniyar MDD.

A ranar Asabar din da ta gabata babban sakatare MDD Ban Ki-moon ya yi suka kan gwajin makamin. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China