Gwamnatin Nigeriya ta fara bincike game da jirgin saman mallakar kamfanin Aero wadda ta samu tangarda a sararin samaniya dauke da fasinjoji a ranar Jumma'an da ta gabata, kamar yadda wani jami'in hukumar kula da jiragen saman kasar ya tabbatar a ranar Talatan nan.
Captain Muhtar Usman, daraktan hukumar kula da jiragen sama ta kasar Nigeriya ya ce, tuni aka fara aiwatar da bincike game da lamarin, yana mai bayanin cewa, kariya da tsaro na ayyukan jiragen sama zai ci gaba da samun cikakken kula.
Jirgin dai an ce yana tashi daga filin saukan jiragen sama na Murtala Muhammed dake Ikko, a cikin mintuna 20 kawai sai jirgin ya samu tangarda, abin da ya sa ya yi saukan gaggawa a Abuja.
Hukumar ta dai ba da tabbaci ga jama'a cewa, ba za'a yi kasa a gwiwwa ba wajen aiwatar da cikakken bincike kan wannan lamari. (Fatimah)