Wani jirgin sama na kamfanin Senegal mai zaman kansa wato Air Senegal ya bace a ranar Asabar a yammacin Dakar, in ji cibiyar kasa dake kula da zirga zirgar jiragen sama na jama'a da kula da yanayi da kamfanin dillancin labarai na kasar Senegal (APS) ya rawaito.
Bayanan ofishin sanya ido na shiyya na cibiyar tsaron zirga zirgar jiragen sama a Afrika da Madagascar sun tabbatar da bacewar jirgin daga na'urar rada da misalin karfe 7 da mintuna 8 na yamma bisa agogon wurin a yammacin birnin Dakar.
Jirgin saman samfurin HS 125 na kan hanyarsa tsakanin Ouagadougou da Dakar bisa tsarin sufuri na kiwon lafiya, kuma yana dauke da mutane bakwai da suka hada da 'yan Senegal su uku, 'yan Aljeriya su biyu da 'dan Congo daya da kuma 'dan kasar Faransa daya. (Maman Ada)