Gwamnatin Nigeriya ta bukaci cikakken bayani daga kamfanin jiragen saman Aero sakamakon wata tangarda da jirginsa ya samu a sararin samaniya ranar Jumma'a.
Kamar yadda kakakin hukumar kula da jiragen sama na kasa NCAA Fan Ndubuoke ya sanar wa manema labarai a Ikko ranar Lahadin nan, jirgin saman kamfanin Aeron mai lamba 180 yana dauke da kusan fasinjoji 120 daga Ikkon zuwa Kaduna, lokacin da dole aka karkata shi zuwa Abuja domin saukan gaggawa.
An ce, jirgin nan ya dagule mintuna 20 da tashin shi daga filin saukan jiragen sama na Murtala Muhammed dake Ikkon.
Sanarwa daga kamfanin jiragen ta tabbatar da cewa, an samu matsalar rashin isasshen iska ne a cikin jirgin, abin da ya sa malfar ba da iska na jirgin suka sauko, kuma ganin cewa jirgin a Abuja ne aka duba ingancin tashin shi, dalilin da ya sa ya yi saukan gaggawa ta can ke nan domin a sake dubawa.
Sai dai kuma kakakin hukumar ta NCAA Fan Ndubuoke ya ce, jirgin da ya samu wannan matsala ba za'a bar shi ya sake tashi ba, har sai an samu cikakken bayanin, da kuma sake tabbatar da ingancin shi na tashi sama da hukumar za ta yi. (Fatimnah)