in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardar MDD ya aike da sakon taya murnar sabuwar shekarar gargajiya ga al'ummar Sinawa
2016-02-07 12:17:00 cri

Magatakardar MDD Ban Ki-Moon a ranar Asabar din nan ya aike da sakon taya murnar sabuwar shekarar gargajiya ga daukacin al'ummar Sinawa, yana mai masu fatan alheri a cikin shekarar wato murnar bikin bazara da zai fara a ranar Litinin din nan 8 ga wannan watan.

A sakon murnan da ya aike ta faifan bidiyo, Mr Ban ya gabatar da kan shi sannan ya ce barka da sabuwar shekarar gargajiya cikin Sinanci.

Shekarar Biri ta zo. Shi kanshi biri ne. Biri dai yana alamanta hazaka, himma da rayuwa mai kyau. Don haka ya ce shekara ce mai kyau dake cike da fata da kuzari.

Ya lura da cewar wannan shekarar har ila yau ita ce ta farko da za'a kaddamar da shirin muradun karni mai dorewa kuma akwai bukatar farawa cikin nasara da shekarar sa'a ta biri.

Magatakardar MDD daga nan sai ya taya al'ummar Sinawa fatan alheri na shekarar biri da Sinanci.

Bikin bazara dai shi ne mafi muhimmanci a kalandar gargajiya ta Sinawa wanda ke kawo iyalai su hadu waje daya da kuma shiga sabon lokaci. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China