in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD tayi na'am da sauya fasalin majalisar dokokin Somali a 2016
2016-01-29 10:08:55 cri
Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya amince da matakin da gwamnatin Somali ta dauka na kafa sabuwar majalisar dokoki a kasar mai bangarori biyu cikin wannan shekarar ta 2016.

Sanarwar ta ambato Mista Ban yana taya shugabacin kasar Somali murna kan wannan mataki data dauka, cewar matakin ya zo ne a lokacin da ya dace kasancewar zai share fagen kafa sabuwar majalisa a daidai lokacin da wa'adin majalisar ta yanzu ke karewa.

Ban, ya yaba, musamman yadda aka baiwa mata da kananan kabilun kasar wakilci, haka kuma aka ware ma mata kashi 30 cikin 100 na kujerun wakilcin a sabuwar majalisar, wanda yayi daidai da yarjejeniyar Mogadishu ta shekarar 2015.

Babban sakataren na MDD ya ce, wannan sanarwa ta biyo bayan tattaunawa da kuma tuntubar juna ne a tsakanin mahukuntan kasar Somali da bangaren majalisa, da shugabannin al'umma da kuma kungiyoyin al'umma, sannan sanarwar ta ce wannan alamu ne dake zama tamkar kafa tubalin samun zaman lafiya a Somali.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China