in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'an MDD 51 sun hallaka a shekarar 2015: Kakakin MDD
2016-01-22 10:05:12 cri
A ranar Alhamis din nan, mai Magana da yawun MDD ya fada cewar kimanin ma'aikatanta 51 ne suka gamu da ajalin su a yayin da suke bakin daga a shekarar 2015, cikin su harda dakarun aikin wanzar da zaman lafiya da kuma jami'ai na farin kaya dake aiki da hukumar ta kasa da kasa.

A wata sanarwar da kungiyar ma'aikatan MDD ta fitar, ta ce mutane 27 da aka hallaka jami'an wanzar da zaman lafiya ne, ciki harda wasu 'yan sanda 2. Sauran mutane 24 da suka rasa rayuka fararen hula ne, cikinsu akwai 'yan kwangila da suka mutu a yayin hare-haren ganganci, kamar yadda kakakin MDD Farhan Haq ya tabbatar da hakan.

Kungiyar ma'akatan MDD tace, mafi yawan haren haren da suka hallaka jami'an sun hada da harin bama bamai, da harba rokoki, da makaman atilare wadanda aka kaddamar kan jami'an, sannan an kashe wasu jam'an ta hanyar hare haren kunar bakin wake, ko bude musu wuta.

MDD tace a shekara ta 2015, an fi samun hasarar rayukan jami'an ne a kasar Mali inda kimanin jami'ai 25 aka hallaka, yayin da aka musu kwantan bauna a lokacin suna tafe a motocin su.

Batun garkuwa da ma'ikatan na MDD yafi kamari ne a Sudan ta Kudu, inda a can ne aka yi garkuwa da wasu jami'an MDD, sannan wasu daga cikinsu sun bace daga doron kasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China