in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabban kasarTogo yayi ratsuwar kama aiki karo na uku
2015-05-04 20:43:19 cri
Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe a ranar litinin din nan yayi rantsuwar kama aiki karo na uku a gaban kotun tsarin mulkin kasar wadda ta sanar da nasarar shi a zaben da aka gudanar ranar 25 ga watan Afrilu inda ya samu kasha 58.77 a cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Gnassingbe ya hau karagar mulkin kasar ne a shekara ta 2005 bayan wani zaben gaggawa sakamakon mutuwar mahaifin sa kuma tsohon shugaban kasar Janar Eyadema Gnassingbe wanda ya yi mulkin kasar na tsawon shekaru 38 wato daga shekara ta 1967 zuwa 2005.

An sake zaben Faure Gnassingbe a karo na biyu a watan Maris na shekara ta 2010 da kashi 60.89 a cikin 100 da kafatanin kuri'un da aka kada inda ya doke abokin hamayyar sa Fabre mai kashi 33.94.( Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China