Togo na hangen samun bunkasuwa da kashi 5.5 cikin 100 tsakanin 2015 da 2018
Kasar Togo za ta samu wani adadin bunkasuwar tattalin arzikin da zai kai kashi 5.5 cikin 100 a tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar 2018, a cewar wata tawagar aiki ta asusun ba da lamuni na duniya IMF. Tawagar ta kai ziyarar aiki a birnin Lome daga ranar 24 ga watan Juli zuwa ranar 6 ga watan Augusta bisa tsarin shawarwarin tuntubar juna. Adadin bunkasuwar zai kara tasiri bisa samar da albakatun noma, ayyukan sufuri da ke da nasaba da kasuwancin kasa da kasa da kuma muhimmancin alfanun kyautatuwar gine gine ababen sufuri na ayyukan tattalin arziki na masu zaman kansu. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku