in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta nuna rashin jin dadinta kan batun kaddamar da tsarin makamai masu linzami na Thaad a kasar Koriya ta kudu
2016-02-08 13:24:36 cri
Kasar Sin ta nuna rashin jin dadinta game da matakin da kasashen Amurka da Koriya ta kudu suka dauka, game da batun tura wata babbar tawaga daga Amurka domin tattaunawa kan batun kaddamar da makamai masu linzami da aka yi wa lakabi da Terminal High Altitude, wato Thaad a yankin Koriya.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta fada a Lahadin nan cewar, sam bai dace ba a yayin da wata kasa ke kokarin kare kanta, wata kasar ta dabam ta dinga yi mata katsalandan.

Hua, ta ce wannan yunkuri na kaddamar da makamai masu linzami na Thaad a yankin, zai kara dagula al'amura a yankin Koriya, wanda kuma hakan babbar barazana ce ga batun zaman lafiyar yankunan gabashin Asiya baki daya, kuma wannan mataki tamkar koma baya ne ga shirin warware takaddamar da ake fuskanta a yankin.

Ta kara da cewa, kamata ya yi kasashen da abin ya shafa su bi matakan da suka dace wajen waraware takaddamar.

A cewar kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Sin, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Liu Zhenmin ya fadayyace matsayin kasar Sin a yayin wata ganawar gaggawa da jakadan Koriya ta kudu a kasar Sin Kim Jang-soo, cewar game da matsayin da Amurka ta dauka, Sin ta bayyana matsayarta shi ne a bi hanyoyi na diplomasiyya domin warware duk wata takaddama. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China