in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan Chelsea Ramires zai sauya sheka zuwa kulub din Chinese Jiangsu
2016-01-26 14:47:08 cri
Dan wasan tsakiya na kulub din Chelsea Ramires, ya fara share fage domin komawa kulub din kasar Sin Jiangsu Suning a kudi da ya kai fam miliyan 25.

Ramires, wanda ya fara wasa da kulub din na Chelsea a shekarar 2010 a kan kudi fam miliyan 18, yanzu haka ya rattaba hannu kan wata sabuwar kwantiragi ta tsawon shekaru hudu tun a watan Oktoba.

Dan wasan mai shekaru 28 da haihuwa dan asalin kasar Brazil, shine zai kasance dan wasan kwallon kafa mafi tsada a kasar Sin da zai yi aiki da kulub din na kasar Sin da zarar an kammala daddalewa kan yarjejeniyar.

Ramires, shi ne zai zama karkashin kulawar tsohon dan wasan tsakiyar Chelsea din Dan Petrescu dan kasar Romaniya, wanda ke horar da 'yan wasan kulub din Jiangsu tun a watan Yulin shekarar data gabata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China