in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Scolari na cikin wadanda ake wa tsammanin horas da kungiyar kasar Sin
2016-02-01 15:14:21 cri


Tsohon kocin kasar Brazil wanda ya dauki kofin duniya na shekarar 2002 tare da kungiyar kasar Luiz Felipe Scolari, na sahun gaba, cikin wadanda ake zaton za su iya samun damar horos da kungiyar kwallon kafar Sin.

Rahotanni na nuna cewa Scolari dan shekaru 67 da haihuwa, wanda kuma ke horas da kungiyar Guangzhou Evergrande ta nan kasar Sin tun cikin watan Yunin bara, na neman wannan matsayi ne shi da tsohon kocin kasar Italiya, wanda shi ma ja jagoranci Italiyan daukar kofin duniya na shekarar 2006 wato Marcello Lippi, da kuma tsohon kocin Atletico Madrid Gregorio Manzano.

Damar daukar sabon kocin na kasar Sin ta samu ne, tun a farkon watan Janairun da ya gabata, bayan da aka sallami kocin kungiyar dan kasar Faransa wato Alain Perrin saboda rashin tabuka wata rawar gani.

Scolari dai ya cimma nasarori masu yawa tare da kungiyar Evergrande, inda a matakin kasa da kasa, kungiyar sa ta zamo ta hudu a gasar kulaflikan duniya da ya gabata, wanda hukumar FIFA ke shiryawa. A gida kuma, kungiyar ta Evergrande ce ta lashe kofin kalubale da aka kammala, da kuma kofin nahiyar Asiya.

Duk da tagomashin da Scolari ke samu a daya hannun ana ganin kocin kungiyar kwallon kafar birnin Shanghai Shenhua Manzano shi ma na iya samun wannan matsayi.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China