Shirin kasar Sin na raya tsoffin sana'o'i ta hanyar yanar gizo ta Intanet da shirinta na raya masana'antu zuwa shekarar 2025 da ke cikin rahoton ayyukan gwamnatin Sin na shekarar bara, ya jawo hankalin sassa daban daban a kasar.
An gabatar da wannan shiri ne a ranar 27 ga watan jiya a yayin taron majalisar gudanarwar kasar Sin kan harkokin yau da kullum, kuma wannan shi ne karo na farko da aka fitar da wata manufa kan yadda za a hade harkokin raya masana'antu da yanar gizo waje guda.
Masana suna ganin cewa, a baya, shirin raya tsoffin sana'o'i ta hanyar amfani da yanar gizo ya fi jawo hankalin sana'ar ba da hidima da sabbin sana'o'i, duk da haka wajibi ne a sanya sana'ar kera kaya cikin wannan shiri. Yanzu majalisar gudanarwar kasar Sin ta tsara wata taswira kan yadda za a aiwatar da tsarin amfani da muhimman bayanai domin magance matsalolin da masana'antun za su iya fuskanta. Don haka ana sa ran cewa, wannan tsari zai kara inganta sana'o'in kasar Sin. (Tasallah Yuan)